Ko ku daina zuwa sansanin NYSC ko kuma mu fara kama ku muna daurewa - Shugaban NYSC ya gargadi 'yan bautar kasar da basu cancanta ba

Ko ku daina zuwa sansanin NYSC ko kuma mu fara kama ku muna daurewa - Shugaban NYSC ya gargadi 'yan bautar kasar da basu cancanta ba

Shuaib Ibrahim, darakta janar na hukumar NYSC, ya gargadi kowani mai digiri da bai cancanta ba da kada ya kuskura ya kai kansa sansanin yan bautar kasa domin za a kama duk wanda ya kai kansa.

Ibrahim yayi gargadin ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, lokacin da shirin ya sabonta alakarsa da kungiyar jami’o’in Najeriya.

Anyi hadin gwiwar ne domin kara inganta tsarin kwasar dalibai da hana masu kwalayen kammala karatu na bogi yin bautar kasa.

A cewar NAN, Shugaban na NYSC ya bayyana cewa tunda ya hau kujerar shugabantar shirin, ya lura cewa wasu ma’aikatun na koro yan bautar kasa kan hujjar cewa basu cancanci koyarwa ba ko kuma cewa wasu basu iya karatu ba.

Domin magance kalubalen, Ibrahim yace shirin ya hada kai da NUC don ganawa da jami’an da ke kula da harkokin dalibai daga yankin Afrika ta yamma da wasu kasashen Afrika.

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Wasu mutane 8 da suka tafi binne dan uwansu da ya mutu a Yola suma sun hadu da ajalinsu a hanya

Ya kuma bayyana cewa shirin ya kama yan bautar kasa na bogi da dama a kwanan nan sannan ya mika su ya yan sanda domin a hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel