Tirkashi: 'Yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yiwa 'yan kungiyar Biafra da suka fito yiwa shugaba Buhari ihu harbin Kan mai uwa da wabi

Tirkashi: 'Yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yiwa 'yan kungiyar Biafra da suka fito yiwa shugaba Buhari ihu harbin Kan mai uwa da wabi

- 'Yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun tarwatsa gungun 'yan kungiyar Biafra da suka fito domin su yiwa shugaba Buhari ihu a lokacin da ya kai ziyara kasar

- Bayan gama kurari na cewa sai sun ci zarafin shugaban kasar idan har ya sake ya sanya kafar shi a kasar ta Afrika ta Kudu, sai gashi suna neman wajen tsira da lafiyar su yayin da 'yan sanda suka sanyo su a gaba

- Idan ba a manta ba shugaban kasar da tawagarsa sun tafi kasar ta Afrika ta Kudu a ranar Larabar nan da ta gabata

Jami'an 'yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yi harbi kan mai uwa da wabi domin tarwatsa wani gungu na 'yan kungiyar Biafra da suka fito suna yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a lokacin da yaje kasar ta Afrika ta Kudu.

'Yan kungiyar dai sunyi alkawarin za su ci zarafin shugaba Buhari idan har ya sake ya sanya kafar shi a kasar ta Afrika ta Kudu.

Sai dai kuma 'yan mintuna kadan bayan wannan kurari na su, sai gashi jami'an hukumar 'yan sandan kasar dake Pretoria sun taka musu birki, inda suka dinga harbin su, hakan yayi sanadiyyar da yawa daga cikinsu suka samu raunuka a jikinsu.

KU KARANTA: An kori wata daliba da ta shiga aji sanye da hijabi a wata makarantar sakandare dake Ibadan

Wannan mataki da hukumar 'yan sandan kasar ta dauka shine ya kawo karshen wannan kurari da 'yan kungiyar Biafra din suke yi, yanzu haka dai sun ranta ana kare don tsira da lafiyarsu.

Idan ba a manta ba shugaban kasar ya tafi kasar ta Afrika ta Kudu ne a ranar Larabar nan da ta gabata tare da tawagarsa, inda yaje domin samun masalaha akan lamarin da ya faru da 'yan Najeriya makonnin da suka gabata a kasar ta Afrika ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel