An kori wata daliba da ta shiga aji sanye da hijabi a wata makarantar sakandare dake Ibadan

An kori wata daliba da ta shiga aji sanye da hijabi a wata makarantar sakandare dake Ibadan

- Wata makarantar sakandare dake Ibadan ta dakatar da wata daliba wacce ta shiga aji sanye da hijabi

- Makarantar dai ta dakatar da dalibar ne na tsawon mako biyu bayan ta kama ta da laifin karya dokar makaranta

- A watannin da suka gabata ne iyayen daliban makarantar suka nemi hukumar makarantar da ta sanya doka akan daliban da suke zuwa makarantar da hijabi

Wata dalibar makarantar sakandare dake Ibadan mai suna Miss Ikhlass Olasubomi Badiru, hukumar makarantar ta dakatar da ita saboda ta sanya hijabi ta je makarantar da shi a watan Yulin da ya gabata.

Idan ba a manta ba watannin da suka gabata iyayen daliban makarantar sun nemi makarantar ta hana dalibai mata sanya hijabi idan za su shiga makarantar.

KU KARANTA: Yadda muka yi dambe da wani melamin bogi da yazo cire min Aljanu lokacin ina budurwa - Laila Ali Othman

A wata wasika da shugaban makarantar mai suna Phebean Olowe ya rubuta a ranar Litinin dinnan da ta gabata, shugaban makarantar ya bayyanawa dalibar cewa makarantar ta dakatar da ita na tsawon mako biyu, kuma za ta tsaya da zuwa makarantar daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa ranar 18 ga watan Oktoba, 2019.

Makarantar dai ta yankewa dalibar hukunci n bayan hukumar makarantar ta kama da laifin karya dokar makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel