Allahu Akbar: Wasu mutane 8 da suka tafi binne dan uwansu da ya mutu a Yola suma sun hadu da ajalinsu a hanya

Allahu Akbar: Wasu mutane 8 da suka tafi binne dan uwansu da ya mutu a Yola suma sun hadu da ajalinsu a hanya

Hatsarin mota ya cika da wasu mutane takwas da ke dauke da gawar wani dan uwansu domin binne shi inda suka rasa ransu a hanyar Numan-Yola a jihar Adamawa.

Majiyarmu ta tattaro a ranar Alhamis cewa hatsarin ya afku ne a daidai Afcott, wata kamfani kusa da Ngurore a karamar hukumar Kudancin Yola, a ranar Laraba.

Kimanin mutane 14 ne suka jikkata.

Majiyoyi sun bayyana cewa hatsarin ya hada da motar dake raka gawa daga Jada ta hanyar Guyuk, inda wata motar Starlet ta doke ta bayan tayi kokarin shan gabanta.

Kwamandan hukumar hana afkuwar hatsarurruka, Mohammed Hussaini ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Ya bayyana cewa tukin ganganci ne ya haddasa lamarin.

Gwamnatin a Wani jawabi da ta saki tace mafi akasarin mutanen yan cocin Lutheran Church of Christ in Nigeria (LCCN) ne.

KU KAANTA KUMA: Allah ya yiwa tsohon shugaban jam'iyyar AD rasuwa yana shekara 89

Gwamna Fintiri na jihar ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

Ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan sannan yayi addu’a Allah ya ji kan mamatan sannan ya ba wadanda suka jikkata lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel