Kashi 90 na motoccin Najeriya ta barauniyar hanya aka shigo da su - Ali

Kashi 90 na motoccin Najeriya ta barauniyar hanya aka shigo da su - Ali

Shugaban hukumar Kwastam ta Najerita, Kwanel Hameed Ali (ritaya) ya ce kashi 90 cikin 100 na motocin da ke Najeriya ta haramtaciyyar hanya wasu hatsabiban mutane suka shigo da su.

Mista Ali ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja a ranar Alhamis inda ya yi ikirarin cewa da yawa cikin motoccin da ke shagunan sayar da motocci a kasar suma ta barauniyar hanya aka shigo da su.

Ya yi bayyanin cewa jami'an hukumar suna kai sumame shagunan sayar da motocci ne a cikin 'yan kwanakin nan domin tabbatar da cewa motoccin da ke shagunan ta halastaciyyar hanya aka shigo da su kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

A cewarsa, Najeriya na bukatar kudin shiga domin yin ayyukan cigaba hakan yasa ya zama dole a karba haraji a kan motoccin da aka shigo da su ba bisa ka'ida ba.

"Muna son muyi amfani da wannan damar mu tabbatar da cewa dukkan motoccin da ke kasar mu son bi ta hannun kwastam wanda hakan ke nufin an biya musu haraji.

"Muna neman kudaden shiga daga ko ina sai kuma ga wasu mutane da ke shigo da motocci amma ba su son biyan haraji.

"Abinda muke yi yanzu, muna zartar da dokar kasa ne kawai wadda ya bamu damar karbar haraji a madadin gwamnatin Najeriiya tare da tabbatar da cewa motoccin da ni da kai zamu siya suna da inganci kuma suna da takardu na ainihi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel