Kwace gidan Saraki: Majalisar jihar Kwara ta yi karin haske

Kwace gidan Saraki: Majalisar jihar Kwara ta yi karin haske

- Majalisar jihar Kwara a cikin 'yan kwanakin nan ta kwace wani gida mallakar Sanata Bukola Saraki

- Majalisar jihar tayi bayanin dalilin da yasa ta kwace gidan

- Majalisar tayi bayanin ne sakamakon wani rahoto da aka wallafa na cewa gwamnatin jihar tana yi wa Saraki bita da kulli

Majalisar jihar Kwara ta bayar da umurnin kwace wani gidan hutawa da aka bawa tsohon gwamnan jihar, Sanata Bukola Saraki.

Majalisa ta ce ta dauki matakin ne domin gidan mallakar gwamnatin jiha ne.

Majalisar ta bakin kakakin ta, Ibrahim Sherif ta ce kyautar da gidan da tsohuwar gwamnatin jihar tayi ya sabawa dokokin jihar.

Majalisar tayi wannan bayanin ne sakamakon wani rahoto da aka wallafa na zargin ta da yi wa Saraki bita da kulli.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

Magoya bayan Saraki suna zargin gwamnatin jihar da musguwanawa tsohon shugaban majalisar dattawan.

"Kyauta irin wannan tayi kama da abinda marigayi Fela Anikulapo ya kira 'tsarin aboki da aboki'.

Sanarwar da majalisar jihar ta fitar ya ce wallafa cikaken bayani kan lamarin da kwamitin gidaje, filaye da cigaban birane na majalisar jihar tayi a kan batun.

"Muna kallubalantar duk wani da ke ganin bita da kulli ake yi ya gabatar da hujja ko shaidan biyan kudi na gidan," inji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel