Dalilan da suka sa gwamnatin jihar Zamfara ta rufe wata makarantar firamare a jihar

Dalilan da suka sa gwamnatin jihar Zamfara ta rufe wata makarantar firamare a jihar

- A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta rufe makarantar Shattima Model primary School tare da dakatar da malamanta

- An gano wasu shafuka na Alkur'ani mai girma ne a cikin shaddar makarantar

- Gwamnan jihar ya ce ba za a lamunci hakan ba, don haka za a zakulo tare da hukunta duka mai hannu a wannan aika-aikar komai matsayinsa

Kwanaki kadan da suka gabata, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya rufe makarantar Shattima Model Primary School dake Gusau tare da dakatar da duk malaman makarantar akan zarginsu da ake da tozarta Alkur'ani mai girma.

Wajen karfe 11 na ranar Juma'ar da ta gabata ne aka ga shafukan Kur'ani mai girma a shaddar makarantar.

KU KARANTA: Mace mai kamar maza: Ta adana kwalin digirinta, ta tsunduma tukin Keke Napep

A takardar da babban daraktan yada labarai na gwamnan, ya ce za a cigaba da rufe makarantar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Gwamnan ya ce, za a gano wadanda suka yi mummunan aikin. Ya kara da kara masu gadi uku-uku a duk makarantun firamare da ke babban birnin jihar.

"Gwamnati zata hukunta duk wanda ta samu da hannu a wannan aika-aikar komai kuwa matsayinsa," in ji shi.

Ya bukaci mutane da su kara sa ido tare da kiyayewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel