Gwamnatin jihar Ekiti ta horar da malamai 3,000

Gwamnatin jihar Ekiti ta horar da malamai 3,000

Kwamishinan ilimin jihar Ekiti, Funso Daramola ya ce kimanin malaman makarantun firamare da sakandare 3,000 ne a baiwa horon hanyoyin koyarwa na zamani a jihar tun daga lokacin da gwamnatinsu ta soma mulkin jihar.

Mr Daramola ya fadi wannan maganar ne a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bikin ranar malamai ta 2019 a Ado-Ekiti.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Ku kwantar da hankalinku, Osinbajo ya lallashi kungiyar ‘yan kwadago

Kwamishinan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Kayode Fayemi za ta cigaba da bunkasa hanyoyin samar da ilimi a jihar Ekiti musamman a fannin horon malaman makarantun jihar.

Ya kuma kara da cewa, wannan yana daga cikin kuduroran Gwamna Fayemi na bai wa ilimi kulawa ta musamman, inda ya ce malamai 60 daga makarantun sakandaren kimiyya da fasaha sun halarci taron sanin makamar aiki a jihar Kano cikin watan Agusta.

Daramola ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatin jihar Ekiti ta riga da ta kammala duk wani shiri domin gudanar da taron cikin armashi da tsanaki na shekarar 2019.

Kwamishinan ya sake cewa: “Kimanin malamai 21,000 na makarantun kudi da na gwamnati ne ake sa ran zasu halarci bikin na bana.”

A karshe kwamishinan ya fadi cewa ilimi shi ne ginshikin cigaba ga ko wace al’umma a don haka wannan dalilin ne ya sanya gwamnatin Fayemi ta bada kulawa ta musamman game da duk wani abinda ya shafi cigaban ilimin jihar.

https://dailynigerian.com/ekiti-trains-3000-teachers/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel