Mafi karancin albashi: Ku kwantar da hankalinku, Osinbajo ya lallashi kungiyar ‘yan kwadago

Mafi karancin albashi: Ku kwantar da hankalinku, Osinbajo ya lallashi kungiyar ‘yan kwadago

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin Shugaba Buhari za ta kaddamar da karin albashi ga ma’aikatan da albashinsu bai kai matakin da sabon mafi karancin albashin yake ba.

Osinbajo ya fadi wannan maganar ne a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 a yayin da yake karbar bakuncin shuwagabannin kungiyar ‘yan kwadago a fadar shugaban kasa ta Villa. Shugaban kungiyar TUC Quadri Olaleye shine ya jagoranci tafiyar tare da ministan kwadago Chris Ngige.

KU KARANTA:Hukumar Kwastam ta fadi adadin kudin ta samu na watan Satumba

Mataimakin shugaban kasan ya jinjinawa kungiyar ‘yan kwadagon inda ya ce: “Zuwanku nan ya tabbatar mana da cewa kun shirya domin yin aiki tare da gwamnatinmu. Ina so ku amince da gwamnatin Buhari, a matsayin wadda kyautatawa ma’aikata ke gaba a cikin kudurorinsa.

“Idan baku manta ba daya daga cikin abinda ya fara yi lokacin da ya amshi gwamnati, shi ne bsi wa gwamnonin jihohi kudin tallafi domin biyan bashi albashin da ma’aikata ke bi.”

Haka kuma Osinbajo ya sake jaddada kudurin gwamnatin Buhari na faranta rayuwar ma’aikata inda ya ce akwai kudaden Paris kulob wanda gwamnatin ba tayi kasa a gwiwa ba wurin raba su ga jihohin Najeriya.

Da kuma yake karin haske game da mafi karancin albashin, Osinbajo ya ce: “Kada kuyi tantama game da Shugaba Buhari, ina so ku kwantar da hankalinku shugaban kasa zai kaddamar da sabon mafi karancin albashi.

“Abinda kawai Shugaban ke da bukata shi ne tattaunawa ta musamman da jagororin kungiyoyin kwadago ta yadda za a kai karshen maganar.” Inji Osinbajo.

https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/355896-minimum-wage-trust-buhari-be-open-minded-osinbajo-tells-workers.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel