Allah ya yiwa tsohon shugaban jam'iyyar AD rasuwa yana shekara 89

Allah ya yiwa tsohon shugaban jam'iyyar AD rasuwa yana shekara 89

Wani tsohon Shugaban jam’iyyar Alliance for Democracy (AD), Sanata Mojisoluwa Akinfewa ya mutu.

Akinfewa wanda ya kasance dan asalin Erin Ijesa dake jihar Osun, ya rasu yana da shekara 89 a gidansa dake Ibadan a ranar Alhamis, 3 ya watan Oktoba.

Da yake tabbatar da mutuwar Akinfewa, wani tsohuwar shugaban jam’iyyar AD a jihar Osun, Hon Olapade Fakunle, yace, tsohon Shugaban na AD ta kasa ya kasance cikin koshin lafiya har zuwa karshen rayuwarsa.

Ya mutu ya bar yaransa da sauran yan’uwa.

An zabi Sanata Akinfewa a 1999 a matsayin sanata mai wakiltan mazabar Osun ta gabas da ke jihar Osun a majalisar dattawa, kar karkashin jam’iyyar AD, sannan ya zama shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)

Kafin lokacin ya kasance tsohon kwamishinan ilimi a karkashin gwamnatin marigayi Bola Ige wanda ya kasance Gwamnan jihar Oyo a wancan lokacin.

An ajiye gawarsa a asibitin Wasley sannan za a sanar da shirye-shiryen binnesa daga baya.

A wani labari na daban, mun ji cewa wani kunkuru mai shekaru 344 wanda aka fi sani da suna Alagba a fadar masarautar Soun dake Ogbomoso ta jihar Oyo ya mutu.

Kunkurun wanda aka yi ittifakin cewa shi ne kunkuru mafi tsufa a Afirka ya mutu ne ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 bayan yayi wata ‘yar gajeruwar jinya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel