Hukumar Kwastam ta fadi adadin kudin ta samu na watan Satumba

Hukumar Kwastam ta fadi adadin kudin ta samu na watan Satumba

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wadda aka fi sani da Nigeria Customs Service (NCS) ta ce biliyan N115 ta samu watan Satumba, inda ta bayyana shi a matsayin kaso mafi tsoka tun bayan da gwamnati ta rufe kan iyakar kasar.

Shugaban hukumar, Kanal Hameed Ali ne ya bada wannan labari a lokacin da yake karbar bakuncin shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole a ofishinsa dake Abuja ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba.

KU KARANTA:Zaben Bayelsa: Faduwar gaba asarar namiji, Oshiomole yayi martani ga Dickson da PDP

Ali ya shaidawan shugaban APC cewa tun bayan rufe kan iyakar Najeriya kudaden shigan hukumar a kullum karuwa suke yi.

Ya kuma kara da cewa, “ba a taba samun kudaden shiga masu yawa ba irin na watan Satumba. Dokar da aka sanya ta rufe kan iyakar kasar nan ta sanya masu fasa kwauri biyan kudaden haraji a bisa tilas.”

A cewar Ali, manufar rufe kan iyakar kasar da gwamnatin tayi shi ne na ta tabbatar da cewa ta na kulle har zuwa sabuwar shekarar 2020.

Bugu da kari, ya sake cewa babban makasudin rufe kan iyakan shi ne domin a tilastawa sauran kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS bin dokokin kungiyar kamar yadda aka tsara su.

Kamar yadda ya ce: “Tsarin kuwa shi ne, kasashen dake makwabtaka da Najeriya su sanya jami’an kwastam a ko wane lokaci su rika rako masu fatauci kayayyaki domin kada su samu damar gujewa biyan kudin shiga.”

A karshe Ali ya kara da cewa, rufe kan iyakar ya taimakawa tsaron Najeriya kasancewar a yanzu haka an samu raguwar kashe-kashe na ba gaira ba dalili da ake fama da su a kwanakin baya.

https://dailynigerian.com/nigerian-customs-generates-n115bn-in-september/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel