Kotu ta yankewa wani tsohon babban sakataren tarayya shekaru 5 a gidan maza

Kotu ta yankewa wani tsohon babban sakataren tarayya shekaru 5 a gidan maza

- Babbar kotu ta musamman a Ikeja, jihar Legas ta yankewa tsohon babban sakataren tarayya hukuncin shekaru 5 a gidan gyaran hali

- Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo ya yanke wannan hukuncin ne bayan da ya kama tsohon babban sakataren da laifin handame kudade har naira miliyan 14

- Tun a shekarar 2017 hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta fara gurfanar da Clement Illoh

A yau Alhamis ne mai shari'a Oluwatoyin Taiwo, da ke babbar kotu ta musamman a Ikeja, jihar Legas, ya yankewa tsohon babban sakataren ma'aikatar kwadago da aiyukan yi, Clement lloh, shekaru 5 a gidan kaso.

An kama tsohon babban sakateren tarayyar ne da laifin kalmashe naira miliyan 14.1 na tsohon shirin Subsidy Reinvestment and Empowerment Programmme (SURE-P).

KU KARANTA: Jami'an Operation Lafiya Dole sun tseratar da mutane 51 da 'yan Boko Haram suka sace

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da lloh tun a shekarar 2017 bayan da ta kamasa da baiwa kansa kwangilar karya da kamfaninsa yayin da yake kula da aiyuakn SURE-P.

An tuhumeshi dsa abubuwa kamar haka: "Cewa kai Clement Illoh wanda aka fi sani da mamallakin kamfanin Clement & Bob, a ranar 28 ga watan Janairu na 2015, lokacin kana matsayin babban sakataren gwamnatin tarayya ka waskar da kudi har naira miliyan 14.176 don amfanin kanka.

"Kudin sun fito ne daga NIMASA. A don haka ne ka aikata laifin da ya ci karo da sashi na 279, sakin layi na farko da kuma sashi na 285, sakin layi na 6 daga cikin dokokin laifukan jihar Legas."

Bayan gurfanar da shi, kotun ta yi zama har sau biyu inda ta kamashi dumu-dumu da laifin da ake zarginsa da shi. Babu bata lokaci aka yanke masa hukuncin da ya dace.

Mai shari'ar ya kara da umartarsa da ya hanzarta biyan kudaden da ya waskar har naira miliyan 14 ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel