EFCC ta gurfanar da tsohon mai bawa Buhari shawara kan zargin almundahar N974m

EFCC ta gurfanar da tsohon mai bawa Buhari shawara kan zargin almundahar N974m

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annti (EFCC) ta gurfanar da tsohon mai bawa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin Neja Delta a gaban kotu kan zargin damfara ta N974m da karkatar da kudade da suka kai $1.9m.

An gurfanar da Brig. Janar Paul Boroh (riyata) ne tare da Hanafi Moriki a gaban Mai shari'a O.O. Goodluck na babban kotun Abuja kan wasu tuhume-tuhume guda tara.

A cikin sanarwar da kakakin EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya fitar, ya ce, "wadanda aka yi karar sun karkatar da N8,601,571; N106,288,445; N12,078,450; N382,800,000; N456,000,000; N9,000,000 da wasu yayin da suke ma'aikatan gwamnati.

A watan Maris din shekarar 2018 ne shugaba Buhari ya sallami Boroh a matsayinsa na shugaban shirin tallafi na tsaffin 'yan tayar da kayan baya na Neja-Delta ya maye gurbinsa da Farfesa Charles Dokubo.

DUBA WANNAN: Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

An ruwaito cewa EFCC da wasu hukumomin tsaro suna bincike a kansa saboda an same shi da miliyoyin kudade da ba a san inda ya samo su ba.

Sai dai bayan karanto musu kararrakin, sun ce basu aikata laifukan ba.

Bayan hakan ne lauyan Boroh, Cif Mike Ozekhome (SAN) ya roki kotu ta bayar da wanda ya ke karewa a beli duba da cewa shine ya kawo kansa kotu duk da rashin lafiya da ya ke fama da ita.

Lauyan wanda ke tuhuma na biyun shima ya nemi kotu ta bayar da wanda ya ke karewa a beli.

Mai shari'ar ya bayar da beli ga Boroh da Moriki kan kudi N2m da N20m.

Kotun ta kuma bukaci su gabatar da wadanda za su tsaya musu guda biyu wadanda ba su gaza mukamin mataimakin direkta ba a aikin gwamnatin tarayya kuma mazauna garin Abuja. Kotun ta kuma ce su mika fasfo dinsu.

Daga bisani, Mai shari'a Goodluck ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 26 da 27 ga watan Nuwamba da kuma ranar 3 da 4 ga watan Disamban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel