Yadda tsohon gwamnan Bauchi ya yi rub da ciki da manyan motoci, da dukiyoyi - Isa Misau

Yadda tsohon gwamnan Bauchi ya yi rub da ciki da manyan motoci, da dukiyoyi - Isa Misau

Kwamitin kwato dukiyoyin sata ta gwamnatin jihar Bauchi tana zargin tsohon gwamnan jihar, Mohammed A Abubakar, da laifin babakere da hanbadan dukiyoyin jihar lokacin da yake karagar mulki. Daily Nigerian ta bada rahoto.

Rahoto ya gabata cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nada kwamiti na musamman domin binciken ayyukan gwamnatin da ta shude.

Shugaban kwamitin, Sanata Isa Misau, ya bayyanawa manema labarai cewa tsohon gwamnan ya sayarwa kansa manyan motocin gwamnati bakwai.

A cewarsa, hakan ya sabawa dokokin saye da sayarwan jihar.

A cewar Sanata Misau, motocin sun kunshi Land Cruiser maras jin harasashi da ya sayarwa kansa N7,800,000.00, sai Land Cruiser da ya sayarwa kansa V8, N2,800,000.00.

Sauran sune: Toyota Hilux biyu da ya sayarwa kansa kowanne N1,050,000, Range Rover (Jeep) 3 da ya sayarwa kansa kudi N2,114,700.00., N2,947,875.00 da N2,114,700.00

KU KARANTA: Gwamnatin za ta sallami ma'aikata muddin ana son ta biyan mafi karancin albashi - Chris Ngige

Misau ya kara da cewa akwai manyan motoci 30 da aka baiwa hadiman gwamna Abubakar amma basu dawo da su ba.

Yace: "Kwamitin ta kwato motoci 15 kuma tana bibiya sauran 15 domin kwatosu. Hakazalika kwamitin na kokarin kwato wasu motoci da gwamnan ya yiwa kansa gwanjo."

Sanata Hamma Misa ya ce tsakanin watan Oktoba 2016 zuwa Mayu 2018, an sace kimanin bilyan 1.4

Asali: Legit.ng

Online view pixel