Gwamnatin za ta sallami ma'aikata muddin ana son ta biyan mafi karancin albashi - Chris Ngige

Gwamnatin za ta sallami ma'aikata muddin ana son ta biyan mafi karancin albashi - Chris Ngige

Ministan kwadago, Chris Ngige, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa bukatar kungiyoyin kwadago na aiwatar da karin kudin mafi karancin albashi zai karawa gwamnatin tarayya nauyin N580 billion a kowani shekara.

Ngige ya ce wannan bukata da shugabannin kwadago keyi bai zai yiwu ba sai dai idan gwamnati za ta rage yawan ma'aikata domin cimma abinda suke so.

Ministan ya ce gwamnatin ba zata iya biyan kudin ba yanzu saboda babbar manufar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari shine inganta albashin kananan ma'aikatan gwamnati daga daraja ta 1 zuwa 6.

Ministan ya bayyana hakan ne yayinda shugabannin kungiyar kwadago United Labour Congress (ULC) karkashin jagorancin Mista Joe Ajeiro suka kawo masa ziyara ofishinsa.

KU KARANTA: Yan bindiga sun dira makaranta a Kaduna, sun yi awon gaba da dalibai mata

Yayinda yake kira ga ma'aikata su fahimci halin da gwamnati ke ciki, Ngige ya jaddada cewa dubi ga yadda tattalin arzikin kasa yake yanzu, karin kudin albashi ba zai yiwu ba.

Ya ce gwamnati na gudun abinda zai kai ta ga sallaman ma'aikata saboda hakan tsanani zai karawa al'umma.

Ngige ya yi kiraga kungiyoyin kwadago su amince da karin da gwamnati ta bayyana cewa za ta iya ga ma'aikata masu darajar 7 zuwa 17 saboda watanni uku kadai rage domin aiwatar da mafi karancin albashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel