Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya titsiye babban manajan hukumar inganta birane na jihar saboda maye gurbin sunayen wasu layyuka a babban birnin jihar da sunansa.

Hakan na cikin wata sanarwa ne mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan, Terver Akase da ya fitar a Makurdi, babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Ortom ya bayar da umurnin dakatar da canja sunayen wasu layyukan da ake yi, ya kuma bukaci a cire sabbin sunayen da aka saka a wasu layyukan.

Gwamnan ya bayar da umurnin mayar da sunan layin Ahmadu Bello Way da aka canja da sunansa.

DUBA WANNAN: Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

Ya kuma bukaci direkta janar da hukumar ya yi masa bayanin dalilin da yasa ya fara wannan aikin sauya sunayen layyyukan ba tare da neman amincewa ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Al'ummar garin suma ba su amince da sauyin sunayen layyukan ba.

Layukan da aka canjawa suna sun hada da - Ahmadu Bello Way zuwa Samuel Ortom Road, Gboko Ring Road zuwa Tony Ijohor Road, Gyado Hospital Road zuwa James Ortese Road.

Saura sun hada da Mkar Road zuwa Iyorchia Ayu Road, St John Road zuwa Makir Dzakpe Way da dai wasu sauran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel