Mulki dole: Tsohon gwamnan APC daga arewa na ta hankoron Buhari ya nada shi shugaban FIRS ta kowacce hanya

Mulki dole: Tsohon gwamnan APC daga arewa na ta hankoron Buhari ya nada shi shugaban FIRS ta kowacce hanya

Lallai babu mamaki a maganar da wasu ke fadi cewa dan siyasa babu mukami a hannunsa tamkar kifi ne da ba ya cikin ruwa. Irin hakan ce yanzu ke faruwa da tsohon gwamnan jam'iyyar APC daga arewa bayan ya sha kaye a zaben gwamna na shekarar 2019.

A wani rahoto da jaridar The Nation ta wallafa ranar Alhamis, ta ce tun bayan gaza samun damar sake lashe zabe a karo na biyu tsohon gwamnan ke hankoron neman mukami mai tsoka a gwamnatin APC da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke jagoranta.

The Nation ta ce yanzu haka wannan tgsohon gwamna ya sako kujerar shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS), Dakta Babatunde Fowler, a gaba.

A cewar The Nation, jama'a da dama sun yi matukar mamakin jin cewa tsohon gwamnan na neman kujerar, saboda rashin ilimin Boko mai zurfi da yake da shi. Sai dai, wasu sun ce gwamnan na neman kujerar ne saboda ya yi ittifakin cewa babu abinda zai nema ya rasa a gwamnatin tarayya matukar ya rike mutanen da suka dace.

DUBA WANNAN: A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7

Jaridar ta ce yanzu haka tsohon gwamnan yana ta kulle-kulle da cuku-cukun neman kujerar shugabancin FIRS tare da fada wa na kusa da shi cewa shine zai maye gurbin Fowler, dan asalin jihar Legas.

Duk da an ce wasu na jikinsa sun ankarar da shi a kan karancin ilimi mai zurfi da kan iya zamar masa barazana, tsohon gwamnan kan sanar da su cewa ba maganar karatu ba ce, magana ce ta siyasa, a saboda haka zai cigaba da neman kujerar ruwa a jallo.

Wani abu da ya kara bawa wasu mamaki shine yadda kayayyen gwamnan ya gaza amfani da matsayinsa wajen inganta bangaren samar da kudaden shiga ga jiharsa a lokacin da yake mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel