Jami'an Operation Lafiya Dole sun tseratar da mutane 51 da 'yan Boko Haram suka sace

Jami'an Operation Lafiya Dole sun tseratar da mutane 51 da 'yan Boko Haram suka sace

- Jami'an operation lafiya dole na rundunar sojin Najeriya sun kubutar da mutane 51 da 'yan ta'adda suka sace

- Jami'an sun cire wasu abubuwa masu fashewa da 'yan ta'addan suka dasa a yankin Buni Gari na karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe

- Sun ceto mutanen tare da kwace motar bindiga daya, bindigogi biyu masu kirar AK47 da kuma bindigar harbo jirgin sama

Jami'an Operation Lafiya Dole na rundunar sojin Najeriya sun tseratar da akalla mutane 51 da 'yan ta'addan Boko Haram suka kwashe a karamar hukumar Gubio ta jihar Barno.

Jami'an sun cire wasu abubuwa masu fashewa da 'yan ta'addan suka dasa a yankin Buni Gari na karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe.

Kamar yadda jami'an suka sanar, mutane 51 na sacesu ne a ranar Talata bayan musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan ta'addan.

KU KARANTA: Dalilan da yasa kungiyoyin kwadago ke barazanar tafiya yajin aiki

Rundunar sojin ta ce, an samu motar bindiga, bindigogi kirar AK-47 guda biyu da bindigar harbo jirgin sama guda daya a wajen 'yan ta'addan.

Rundunar 'yan sandan sun kiyaye kiran da shugabansu, Tukur Buratai ya yi garesu na tabbatar da zaman lafiya da lumana a fadin kasar nan.

Jami'in yada labarai na rundunar, Col Aminu Iliyasu, ya kara da cewa, "Binciken farko na lamarin ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin da kuma wata kungiyar taimakon kai da kai da ke aiki a arewa maso gabas din na samun labarai a lokuta da dama."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel