Wata sabuwa: Sanatan Najeriya ya nemi a rage yawan yan majalisa da kaso 70 don rage kashe kudi

Wata sabuwa: Sanatan Najeriya ya nemi a rage yawan yan majalisa da kaso 70 don rage kashe kudi

Rochas Okorocha, sanata mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, ya yi bukaci ayi ragi wajen gudanar da ayyukan majalisar.

Ya bayyana cewa ana iya yin haka ne idan aka rage yawan adadin yan majalisa masu wakiltan kowace jiha a majalisar dattawa zuwa daya, sannan a Rochas Okorocha, sanata mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, ya yi bukaci ayi ragi wajen gudanar da ayyukan majalisar.rage na majalisar wakilai zuwa uku.

Wannan zai mayar adadin yan majalisan tarayya zuwa 146 daga guda 469 da ake dasu, wannan yana nufin za a samu ragowar kashi 69.

Ya fadi haka ne a zauren majalisar dattawa a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba yayin da yake mayar da martani kan rahoton da kwamitin majalisar kan kudi da tsarin kasa ta gabatar na kasafin kudin 2020-2023.

Mista Okorocha yace, “Mafita zamu nema ba kara janyo matsaloli ga majalisar zartarwa ba. Mu suke jira. Me muke da shi da zamu nuna wanda ya banbanta? A takaice dai butun kudi muke ta magana akai, bamu da isasshen kudin biyan bukatun yan Najeriya, samar da ayyuka da kuma samar da abinci a teburin talakawa."

KU KARANTA KUMA: Babu albashin sabbin ma'aikata 30,000 da za a dauka a cikin kasafin 2020 - Lawan

Mista Okorocha ya goyi bayan jerin yan Najeriya dake son a rage yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da ayyukan majalisar.

A kwanan nan ne kungiyoyi da dama suka nuna adawa akan shirin kashe biliyoyin nairori wajen siya wa yan majalisa motoci duk da mawuyacin yanayi da tattalin arzikin da gwamnatin ke fama da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel