A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7

A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7

Ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa ya jagoranci rufe layukan wayar hannu marasa rijitsa fiye da miliyan tara da ke fadin Najeriya.

Da yake jawabi ranar Alhamis yayin wani taro da wakilan bankin duniya a ofishinsa, Pantami ya ce ya yi abinda aka dauka ba zai yiwu ba a shekaru bakwai da suka gabata.

"Tsawon shekaru bakwai kenan ana fama da matsalar layukan wayar hannu marasa rijista, amma a wannan karon, cikin kwanaki 45 kacal, mun warware wannan matsalar.

"Yawancin kamfanonin sadarwa sun nemi su gana da ni, amma na ki amincewa tare da fada musu su koma kan tsarin da ya dace," a cewar minstan.

Yayin ganawar, Pantami ya bayyana muhimman bangarorin da ma'aikatarsa za ta mayar da hankali a kansu.

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa kungiyar SERAP damar tilasta hukumar CCB ta wallafa kadarorin Buhari da gwamnoni

Daga cikin bangarorin da ya ambata akwai inganta tattalin arziki ta hanyar fasaha, bawa fasahar da aka kirkira a cikin gida muhimmanci, samar da aiyuka ta hanyar fasahar zamani, ilimantar da jama'a a kan ilimin fasahar zamani da sauransu.

Wakilan bankin duniya sun ziyarci Pantami ne bisa jagorancin darektan bankin a Najeriya, Shubhan Chaudhuri.

Minsitan ya ce Allah ya albarkaci Najeriya da yawan matasa da ke amfani da fasahar zamani tare da bayyana cewa zai yi amfani da matsayinsa wajen bullo da tsare-tsare da zasu bawa irin wadanann dandazon matasa damar samun aiyuka a bangaren fasahar zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel