Shugaban NYSC ya bayyana alakar da ke tsakanin albashin ma'aikata da alawus din 'yan bautar

Shugaban NYSC ya bayyana alakar da ke tsakanin albashin ma'aikata da alawus din 'yan bautar

Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, darakta janar na hukumar NYSC yace kudin alawus din yan bautar kasa na wata-wata na jone da kudin kasafin kudin kasar sannan kuma karin zai ta’allaka akan sabon kasafin kudin.

Ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Najeriya da ke Abuja a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba.

Ibrahim, wanda ya bayar da tabbacin cewa yan bautar kasa zasu samu karin albashi a duk lokacin da aka samu kari a mafi karancin albashin na kasa, ya kara da cewa “shirin na kuma tunanin kara karfi da tasiri.”

Ya roki masu diban ma’aikata da su kula da jin dadin yan bautar kasa tare da basu kula na musamman.

Yace yan bautar kasa za su amfana kai tsaye.

KU KARANTA KUMA: Al’umman garuruwan Zamfara sun shiga halin fargaba yayinda yan bindiga suka kai mamaya yankin

Shugaban na NYSC sun bukaci masu diban ma’aikata da kada su ki amsar yan bautar kasan da aka tura kamfanoninsu.

Ya kara da cewa shirin zai samar da hanyoyin tallafawa gwamnatin tarayya wajen daukar naiyin NYSC ta fannin Kudi, duba ga yawan yan bautar kasa da ake kwasa duk shekara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel