El-Rufai ya yi magana game da 'yan matan da aka sace a makaranta a Kaduna

El-Rufai ya yi magana game da 'yan matan da aka sace a makaranta a Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayar da tabbacin cewa ana yin duk mai yiwuwa domin ganin an ceto dalibai shida da malaman Engravers College, Kakau Daji a karamar hukumar Chikun na jihar da aka sace.

Kwamishinan tsaro da ayyukan cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayar da wannan tabbacin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin jihar tayi Allah wadai da wannan mummunan abinda aka aikata na shiga hakkin dalibai kanana da malaman da ke koyar da su.

DUBA WANNAN: Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

A cewarsa: "Gwamna Nasir El-Rufai ya aike da tawagar gwamnati zuwa unguwar da aka sace daliban domin tabbatar musu cewa hukumomin tsaro suna aiki don ganin sun ceto wadanda aka sace.

"Kwamishinan tsaro da ayyukan cikin gida Samuel Aruwan ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tare da jami'an tsaro.

"Kwamishinan ya yi magana da iyayen yaran da ma'aikatan makarantan inda ya tabbatar musu cewa za ayi duk mai yiwuwa domin ceto wadanda aka sace tare da hukunta wadanda suka aikata ta'asar.

"Za a rika sanar da iyayen yaran da hukumar makarantar yadda abubuwa ke tafiya a lokutan da suka dace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel