Babu albashin sabbin ma'aikata 30,000 da za a dauka a cikin kasafin 2020 - Lawan

Babu albashin sabbin ma'aikata 30,000 da za a dauka a cikin kasafin 2020 - Lawan

Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin tarayya kan kudi da tsare-tsaren kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, ta gabatar da rahoton ta kan tsare-tsaren kasafin kudi na 2020-2022 a zauren majalisar dattawa.

Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin tarayya bata sanya albashin jami’an da take shirin dauka a hukumomin soji, yan sanda, da sauran hukumomin tsaro a sabon shekara ba a takardun.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kudi, Solomon Adeola, ya kuma ce kwamitin hadin gwiwar ya yaba da tsayar da dala 57 kowace ganga a matsayin na mai.

Daga cikin abin da Majalisar ta yi na’am da shi akwai amincewa da Naira tiriliyan 1.5 a matsayin kudin da Najeriya za ta aro a shekara mai zuwa bayan an gano wasu hanyoyin shigan kudi ta kwastam.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa yau 3 ga Watan Oktoban 2019 ne Majalisar Najeriya ta amince da shirin matsakaicin tsarin tattalin arzikin Najeriya. Majalisar dattawa da wakilan kasar sun hadu sun amince da wannan shiri.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin kwamishinan Bayelsa

Kamar yadda mu ka samu labari daga Manema labarai a Yau Alhamis, bayan yin na’am da rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘yan majalisar sun kawo sabon labari a kasafin shekarar badi. ‘Yan Majalisar tarayyar sun yanke abin da Najeriya za ta kashe a 2020 a kan Naira Tiriliyan 10.729.

Abin da gwamnatin tarayya ta shugaba Buhari ta yanke da farko shi ne Naira Tiriliyan 10.002.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel