Kotun koli ta yi fatali da wata kara mai kalubalantar nasarar shugaba Buhari

Kotun koli ta yi fatali da wata kara mai kalubalantar nasarar shugaba Buhari

- Kotun koli ta yi fatali da daukaka karar jam'iyyar HDP da dan takararta, Ambrose Owuru suka yi

- Karar na kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, INEC da jam'iyyar APC

- Kotun ta soke karar ne sakamakon daukaka karar har sau biyu da jam'iyyar ta yi kuma ba a kan lokaci ba

Kotun koli ta soke daukaka karar da jam'iyyar HDP da Ambrose Owuru, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar suka yi.

Jam'iyyar HDP da dan takararta sun shigar da karar da ke kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ya gabata a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Alkalan biyar da suka saurari shari'ar sun samu jagorancin Mary Odili ne a ranar Alhamis. Tuni kuwa suka yi fatali da karar saboda masu karar sun shigar da ita fiye da sau daya.

KU KARANTA: Dalilan da yasa kungiyoyin kwadago ke barazanar tafiya yajin aiki

"Daukaka karar har sau biyu da masu daukaka kara suka yi bashi da nasaba da doka a don haka ne ba zamu yi amfani da shi ba," cewar Odili.

Alkalan sun ce masu daukaka karar sun gaza daukaka ta tun ranar 22 ga watan Augusta, wanda hakan yasa aka soketa.

Kotun ta ce, kotun sauraron kararrakin zabe ta kori karar ne ta yadda ya dace, a don haka ne, "babu daukaka kara".

Wole Olanipekun, lauyan Buhari, Yunus Usman, lauyan INEC da Lateef Fagbemi, lauyan APC sun ce daukaka karar da masu karar suka yi bata dace ba saboda har kashi biyu suka yi.

A maida martanin da lauyan HDP, Isaac Udoka ya yi, ya musanta zargin kotun. Ya ce a ranar 28 ga watan Augusta suka daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel