Zargin badakalar N2.5bn: Rashin bayyanar ministan Buhari a kotu ya kawo tsaiko a shari'a

Zargin badakalar N2.5bn: Rashin bayyanar ministan Buhari a kotu ya kawo tsaiko a shari'a

Rashin bayyanar minstan yada labarai da ala'adu, Lai Mohammed, a kotu ranar Laraba, ya kawo tsaiko a shari'ar da ake tuhumar babban darektan hukumar kula da tashoshin sadar wa (NBC), Ishaq Kawu, da almubazzaranci da kudin gwamnatin tarayya da yawansu ya kai biliyan N2.5 da sunan wani aiki da aka yi wa lakabi da 'Digital Switch-Over Programme'.

Hukumar yaki da cin hanci da rasha wa a tsakanin ma'aikatan gwamnati da zababbu (ICPC), ita ce ta gurfanar da Kawu.

A wani jawabi da Rasheedat Okoduwa, kakakin ICPC, ta fitar, ta ce Ministan na daga cikin wadanda zasu bayar da shaida a gaban kotun saboda rawar da ya taka a badakalar da ake tuhumar Kawu da tafka wa.

Jawabin ya kara da cewa an tsammanin Ministan zai bayyana a gaban kotun domin bayyana rawar da ya taka a cikin badakalar da sunansa ya fito kuru-kuru.

Jawabin na cewa, "ICPC ta gurfanar da Kawu, shugaban kamfanin sadar wa na 'Pinnacle Communictions Limited' da wasu ma'aikatan kamfaninsa saboda yaudarar Ministan yada labarai wajen amince wa da sakin makudan kudin wani aiki zuwa kamfaninsa.

"A cikin jawabin da ya aiko mana, Mohammed ya ce Kawu ya yaudare shi wajen amincewa da bayar da kwangilar ga kamfaninsa. Amma da aka dawo gaban kotu domin cigaba da saurarn karar a ranar Laraba, sai aka sanar da kotu cewa Ministan ba zai samu damar halartar kotun ba saboda wanin aikin kasa na gagga wa da ya taso masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel