Badakkalar N84m: EFCC ta kama jami’an INEC guda 4 a jihar Zamfara

Badakkalar N84m: EFCC ta kama jami’an INEC guda 4 a jihar Zamfara

Reshen hukumar yaki da cin-hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC na jihar Sokoto, ta damke jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC hudu inda ake zarginsu da handame naira miliyan 84.

Mutanen da aka kaman kuwa su ne, Hassan Sidi Aliyu (Sakataren gudanarwa), Hussain Jafar (Mai kula da ayyuka na musamman), Abdullahi Yusuf Abubakar (Ma’aji) da kuma Abdulmumin Usman.

KU KARANTA:Gwamnatin Kaduna ta soma raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 230,000 ‘yan sakandare

Jaridar Punch ta kawo mana labarin cewa wani Abdullahi Nasiru ne ya rubuta korafi zuwa ga hukumar EFCC inda yake kalubalantar hukumar INEC bisa tauye masu wasu hakkokansu na aikin zaben shugaban kasa da gwamna da suka yi a jihar Zamfara.

Abdullahi Nasiru ya bayyana a cikin korafinsa cewa wadanda aka dauka a matsayin sojojin haya domin yin aikin zaben an hana su N6,000 kudin zirga-zirga.

Ya kuma kara da cewa kudin da hukumar ta biyasu ya sha bamban da abinda aka biya wadanda ke wasu jihohin. INEC ta biya sojojin hayan naira 9,000 ga ko wane mutum daya yayin da sauran johohi kamar Sokoto aka biyasu N12,000.

“Bincike ya tabbatar mana da cewa mutum 10,500 da suka yiwa hukumar INEC babu ko daya daga cikinsu da aka biya hakkinsa, wanda kudin ne jimillarsu ya kama miliyan N84.”

Haka kuma hukumar EFCC ta bamu tabbacin cewa ta cigaba da bincike game da yadda wannnan badakkalar take, sannan kuma ta kara da cewa da zarar binciken ya kammala za a tura da wadanda ake zargin zuwa kotu domin su fuskanci shari’a.

https://punchng.com/efcc-arrests-zamfara-inec-officials-over-n84m-alleged-fraud/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel