Gwamnatin Kaduna ta soma raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 230,000 ‘yan sakandare

Gwamnatin Kaduna ta soma raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 230,000 ‘yan sakandare

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta soma rabon kayan makaranta wato ‘uniform’ kyauta ga daliban sakandare 230,000 a fadin jihar.

Kwamishinan ilimin jihar Kaduna, Dr Shehu Makarfi ne ya bada wannan sanarwa ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 a Makarantar sakandaren Kachia a lokacin rabon kayayyakin.

KU KARANTA:Hukumar NDLEA ta damke masu sayarwa ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi a Jalingo

Ya ce dukkanin wata makarantar gwamnatin dake jihar za ta samu kayan kuma kyauta ne ba wai saye za ayi ba. Ya kuma kara da cewa rabon kayan ya kasance daya daga cikin kokarin gwamnatin Kaduna na tabbatar da cewa yara sun samu ilimi mai nagarta.

Haka kuma, kwamishinan ya kara da cewa, ba kayan makaranta kadai gwamnati ke badawa ba hadda littatafan karatu, malamai masu hazaka, kujerun zama domin yin karatu da sauran kayyakan koyarwa na zamani.

Makarfi ya ce: “Gwamnati za ta cigaba da yin kokarin ganin ta inganta yanayin makarantun sakandare sama da 500 a jihar nan.”

Kwamishinan ya fadi cewa, gwamnati na sane da karancin malamai managarta a makarantun sakandaren jihar.

“A don haka ina mai tabbatar maku da cewa nan bada jimawa ba hukumar tantance malamai wato Teachers Service Board za ta kammala daukar malamai 7,600 na makarantun sakandare.

“Ina kuma so nayi amfani da wannan damar domin yin kira a gareku na ku rika tura diyanku zuwa makaranta domin inganta rayuwarsu, ta hanyar samun ilimin da za su iya dogaro ga kawunansu.” Inji Makarfi.

A bangare guda kuwa, da yake janyo hankali dalibai mata bisa muhimmancin neman ilimi, kwamishinan ya ce gwamnati na daukan nauyin karatunsu zuwa kasar waje domin karantar ilimin kiwon lafiya.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/kaduna-govt-distributes-230000-free-uniforms-to-secondary-school-students/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel