Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin kwamishinan Bayelsa

Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin kwamishinan Bayelsa

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Cif George Agbabou Week, mahaifin kwamishinan noma na jihar Bayelsa, Mista Doodei Week.

Anyi gakuwa dashi ne a gidansa da ke Ayama-Ijaw a karamar hukumar Kudancin Ijaw da ke jihar.

Lamarin ya afku ne a safiya ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba.

A bangae guda wasu yan bindiga sun fasa makarantar sakandare a jihar Kaduna cikin dare inda sukayi garkuwa da dalibai mata shida da malamai biyu. Premium Times ta bada rahoto.

Yan bindigan sun dira kwalegin Engravers dake unguwar Sabo, karamar hukumar Chikun misalin karfe 12:10 na dare, ma'ajin makarantan Elvis Allah-Yaro ya bayyanawa manema labarai.

Wata mahaifya ta bayyana cewa akwai yaranta biyu cikin wadanda aka sace.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban kasar jumhuriyar Benin ya zargi Saudiyya da Qatar da daukar nauyin Boko Haram

Ya kara da cewa kwamishanan harkokin tsaron cikin Kaduna, Samuel Aruwan, ya hallara a makarantan kuma yana baiwa jami'an tsaro goyon baya.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Abubakar Sabo, bai yi tsokaci akan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel