Kotu ta bawa kungiyar SERAP damar tilasta hukumar CCB ta wallafa kadarorin Buhari da gwamnoni

Kotu ta bawa kungiyar SERAP damar tilasta hukumar CCB ta wallafa kadarorin Buhari da gwamnoni

Wata kotun tarayyya da ke zamanta a yankin Ikoyi, jihar Legas, ta bawa wata kungiya mai rajin kare hakkin jama'a da tilasta yin gaskiya (SERAP) damar tilasta hukumar tattara wa da adana bayanan kadarorin ma'aikan gwamnati da masu rike da zababbun shugabanni (CCB) domin ta saki cikakken bayanan kadarorin tsofin shugabannin kasa da gwamnoni tun bawan dawowa mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

Alkalin kotun, Jastis Muslim Hassan, ya bawa kungiyar SERAP damar ne bayan ya kammala sauroron hujjojin da lauyansu, Adelanke Aremo, ya gabatar a gabansa.

Da yake yanke hukunci, Jastis Muslim ya ce, "bayan duba na tsanaki a kan bukatar da SERAP suka gabatar, wacce ta kunshi shaidu da bayanai kwarara, na gamsu cewa akwai bukatar a basu dama, a saboda haka na amince da bukatarsu.''

A cikin takardar korafi mai lamba FHC/L/CS/1019/2019 da kungiyar SERAP ta shigar a gaban kotun, ta kalubalanci ikirarin hukumar CCB a kan cewa ba zata iya bayyana bayanan dukiyoyin tsofin shugabannin kasa da gwamnoni ba, tare da kafa hujja da cewa yin hakan zai zama tamkar bayyana sirrinsu.

DUBA WANNAN: Kotu ta girgiza Kana wa, ta ce babu hannun Gawuna da Murtala Garo a yaga sakamakon zaben mazabar Gama

SERAP ta bukaci kotu ta bayar da umarnin tilasta hukumar CCB ta bayar da bayanan kadarorin tsofin shugabannin kasa da gwamnoni tun daga shekarar 1999.

Kungiyar ta ce bayyana bayanan kadarorin shugabanni zai kara kara kawo gaskiya da yarda a tsakanin jama'a da shugabanninsu.

Tun da farko, kungiyar SERAP ta aike da bukatar neman CCB ta bayyana bayanan kadarorin tsofin shugabannin kasa da gwamnoni, amma sai hukumar ta yi kememe tare da yin burus da wannan bukata, lamarin da yasa SERAP ta nufi kotu domin neman ta tilasta CCB sakin bayanan bisa dogaro da dokar neman sahihan bayanai ta kasa (FOIB).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel