Majalisar Tarayya ta kara kasafin 2020 daga Tiriliyan 10.002 zuwa 10.729

Majalisar Tarayya ta kara kasafin 2020 daga Tiriliyan 10.002 zuwa 10.729

A yau 3 ga Watan Oktoban 2019 ne Majalisar Najeriya ta amince da shirin matsakaicin tsarin tattalin arzikin Najeriya. Majalisar dattawa da wakilan kasar sun hadu sun amince da wannan shiri.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Manema labarai a Yau Alhamis, bayan yin na’am da rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘yan majalisar sun kawo sabon labari a kasafin shekarar badi.

‘Yan Majalisar tarayyar sun yanke abin da Najeriya za ta kashe a 2020 a kan Naira Tiriliyan 10.729. Abin da gwamnatin tarayya ta shugaba Buhari ta yanke da farko shi ne Naira Tiriliyan 10.002.

Majalisar ta na so a kara Naira biliyan 729 daga cikin abin da Najeriya za ta kashe a shekara mai zuwa ne domin a dauke nauyin wasu hidindimu. Kwamitin kasafi da tattali su ka yanke wannan matsaya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yi sammakon gabatar da kasafin kudin 2020

Daga cikin abin da Majalisar ta yi na’am da shi akwai amincewa da Naira tiriliyan 1.5 a matsayin kudin da Najeriya za ta aro a shekara mai zuwa bayan an gano wasu hanyoyin shigan kudi ta kwastam.

Bayan dogon lokaci, Sanatoci sun amince da kusan duk abin da shugaba Muhammadu Buhari yake bukata a takardun MTEF wanda za ayi aiki da shi a Najeriya daga shekarar 2020 zuwa har 2020.

Daga cikin inda majalisar ta yi kari akwai bangaren tsaro inda shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya nuna cewa ya kamata a kara warewa sha’anin tsaro kaso saboda halin da ake ciki a yau.

Haka zalika majalisar dattawan ta bayyana cewa ba a ware albashin da za a rika biyan sababbin jami’an tsaroa sojoji da ‘yan sandan da ake sa ran dauka a cikin wadannan takardun kasafin kudi ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel