Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a makon gobe

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a makon gobe

Yanzu nan labari ya ke zuwa mana cewa an shirya rana da lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a gaban 'yan majalisa.

Kamar yadda Jaridun kasar nan su ka samu rahoto, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da wannan ta bakin Kakakin Sanatocin a yau dinnan Alhamis, 3 ga Watan Oktoban 2019.

Sanata Adedayo Adeyeye ya shaidawa Manema labarai cewa shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana a gabansu ne da kundin kasafin kudin Najeriya na shekarar 200 a makon gobe.

Majalisar dattawan ta sa Ranar Talata wanda zai kasance 8 ga Watan Oktoban 2019 a matsayin Ranar da za a gabatar da kasafin kudin. Za ayi wannan zama ne da karfe 2:00 na rana.

KU KARANTA: Buhari ya tafi kasar Afrika ta Kudu inda zai yi kwana uku

Hanzari da za ayi wannan karo ya na cikin kokarin da shugaba Buhari ya ke yi na ganin an dawo da amfani da tsarin kasafin kudi daga Watan Junairu zuwa Disamba a gwamnatin Najeriya.

Kamar yadda aka saba a Najeriya, ‘yan majalisar wakilai da Takwarorinsu na dattawa za su karbi shugaban kasar a babban zauren majalisar wakilai da ke babban birnin tarayya na Abuja.

Kafin nan kuma mun ji labari cewa majalisa ta na so a kara biliyoyin kudi a cikin kasafin kudin kasar. ‘Yan Majalisar sun bada shawarar a kashe fiye da Tiriliyan 10 a shekara mai zuwa.

Haka zalika ‘yan majalisar tarayyar sun amince da kiyasin farashin gangar mai a kan Dala 57 yayin da ake sa ran hako ganga miliyan 2.18 duk rana da kuma farashin Dala a kan N305.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel