Tsohon Shugaban kasar jumhuriyar Benin ya zargi Saudiyya da Qatar da daukar nauyin Boko Haram

Tsohon Shugaban kasar jumhuriyar Benin ya zargi Saudiyya da Qatar da daukar nauyin Boko Haram

Nicephore Soglo, tsohon shugaban jumhuriyyar Benin ya zargi kasashen Saudi da Qatar da samar da daukar nauyyin kungiyar yan ta'addan Boko Haram ta hanyar basu kudi.

Kamar dai yadda kuka sani Boko Haram ta samu daukaka har ma ta zama barazana ga yankin yanmacin Afurka.

Soglo Wanda yayi madana a taron constitutional term limits summit a Naimey, jumhuriyyar Nijar yace dole yan Afrika su tashi tsaye su kuma hada kai don samar da mafita ga matsalolin kansu.

Yace dole nahiyar Afrika, musamman yankin Yammacin Afrika tayi aiki don ganin ta magance matsalolinta da kuma cewa hakki ne akanta ta tantance abokanta na kwarai.

Yace: “Abokanmu daga kasashen a Saudiyya da Qatar ne ke daukar nauyin Boko Haram. Shin mu abokai ne ko akasin haka? Mu fada ma kanmu gaskiya. Ya zama dole mu tsaya tare.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi kira ga ba yan Najeriya da kasashen waje kariya a Afrika ta Kudu

“Ina da yakinin zamuyi nasara idan muka tashi tare.”

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron wanda cibiyar damokradiya kasa ta NDI ta shirya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel