Al’umman garuruwan Zamfara sun shiga halin fargaba yayinda yan bindiga suka kai mamaya yankin

Al’umman garuruwan Zamfara sun shiga halin fargaba yayinda yan bindiga suka kai mamaya yankin

Al’umman kananan hukumomin Anka da Maru dake jihar Zamfara a ranar Talata, sun kasance cikin halin fargaba a lokacin da dururuwan yan bindiga suka kai farmaki yankin, inda suka yi sace sace.

Mazauna yankin sun ce yan bindigan na kan dawowa ne daga sansaninsu a jihar Neja.

Al’umman yankin sun ce fiye da yan bindiga 500 sanye da kayan sojoji da bindigogin AK47 sun tsaya ne a mararraban Mayanchi a karamar hukumar Maru, inda suka yi fashi a gidan mai da kuma fashe-fashen shaguna a kauyen.

Wani mazaunin kauyen wanda yayi magana ba tare da bayyana sunansa ba yace, “Ko da yake yan bindigan basu kai mana hari ba, sun kasance suna tafiya ne a kan mashina wanda hakan ya razana al’umman. Duk da haka sun yi fashi a gidan mai, da kuma sace-sace a shaguna. Wasu mazauna yankin cikin tsoro na ta yabon yan bindigan.”

Wata majiya tace yan bindigan sun zo ne daga jejin Anka, inda suka sace wayoyin jama'a sannan da ba’a cewan yarjejeniyar da aka kulla a Zamfara tsakanin yan bindiga da gwamnatin ”ya hana su kashe kashe ne amman bai hana su sata ba.

A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunan yan sandan Zamfara, Muhammad Shehu, yace lamarin baya da dangantaka da Boko Haram da ta addabi yankin arewa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi kira ga ba yan Najeriya da kasashen waje kariya a Afrika ta Kudu

“Wasu tubabbun yan bindiga ne dake wucewa ta yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

“Wata kungiyar yan bindiga ne da suka halarci wata ganawa kan yadda za su yi maganin wasu tsagerun yan bindiga dake cikinsu wanda suka samu matsala day an kasuwa a yankin. An magance lamarin tsakanin kungiyoyin da yan kasuwan. Ba a rasa rai ko jikkata ba,” inji Mista Shehu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel