Tashin hankali: Dan shekara 19 ya yi garkuwa da karamin yaro, ya bukaci kudin fansa N3.5m

Tashin hankali: Dan shekara 19 ya yi garkuwa da karamin yaro, ya bukaci kudin fansa N3.5m

Hukumar yan sandan jihar Gombe ta damke wani matashi dan shekara 19, Mohammed Sani Adamu, mazaunin Gabukka quaters kan zargin garkuwa da wani yaro mai shekaru 7 da haihuwa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Obed Maru Malum, ta bayyanawa manema labarai cewa jami'an SARS sun damke matashin ne a ranar 23 ga Satumba, kwanaki uku bayan ya sace yaron.

Ta ce ya yi garkuwa da yaron ne a ranar Juma'a, 20 ga watan Satumba a wani Masallaci dake Kumbiya-Kumbiya yayinda yaron ke alwala.

Daga baya ya kira mahaifin yaron, Malam Abubakar, kuma ya bukaci kudin fansan N3.5 million kafin ya sakeshi.

KU KARANTA: Mutane 6 da Allah ke karban addu'ansu a koda yaushe

Tace: "Da ya lura cewa ba zamu biya kudin fansan ba, sai ya kira yayansa mai suna Aminu Babayi inda ya fada masa cewa ya tsinci yaron da aka ce an sace a Gabbuka."

"Yayan ya bukaceshi ya kawo yaron saboda dangin su gode masa. Amma sai mahaifin ya gano cewa lamban wayan da akayi amfani da shi wajen tambayan kudin fansa daya ne da na wanda ya dawo da yaron."

A lokacin, sai aka kaiwa hukumar SARS kara kuma suka damke yaron yayinda ya kawo yaron."

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, a ziyarar da ya kai kasar domin tattaunawa da takwararsa kan kisan yan Najeriya da wasu bakaken fata a kasar.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya da wasu kasashen Afrika a kasar Afrika ta kudu, ya yi kira da gwamnatin kasar ta aiwatar da matakan da aka zayyana domin kiyaye gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel