Ban yi danasanin amsar kaye daga wajen Buhari ba - Jonathan

Ban yi danasanin amsar kaye daga wajen Buhari ba - Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yace bai yi nadamar amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 ba, wanda yayi sanadiyar kawo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan mulki ba.

Jonathan wanda ya kasance shugaba mai mulki a waccan lokacin ya samu kuri’u 12,853,162 kimanin kuri’u miliyan 2.5 kasa da na shugaba Buhari wanda ya samu 15,424,921.

Ya kafa tarihi a lokacin da ya kira Buhari, tun ma kafin a kammala hada sakamakon zaben, inda ya amince da faduwarsa a zaben.

Yayin da yake mayar da martani ga tambayar cewa ko yayi nadama kan sakamakon zaben 2015, ganin yanda al’amura suka yi ta tafiya cikin shekaru hudu da suka gabata, tsohon shugaban kasar yace bai yi nadama akan hukuncin da ya yanke ba saboda sadaukarwa ne ga damokradiyyar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigon jam’iyyar APC ya koka akan kunnowar rikici

“Ban taba yin nadama ba har zuwa yanzu, ba tare da la’akari da yanayin al’amura ba, ban yi nadama ba saboda matakin da na dauka zai cigaba da inganta duk wani tattaunawa da ya shafi siyasa, ba a Najeriya ba kadai amman har a fadin nahiyar Afrika”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel