Wani babban jigon jam’iyyar APC ya koka akan kunnowar rikici

Wani babban jigon jam’iyyar APC ya koka akan kunnowar rikici

Mataimakin babban sakataren labarai na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Mista Yekini Nabena ya koka kan abunda ya bayyana a matsayin ruruwar wutar rikicin siyasa a jihar Bayelsa, gabannin zaben gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Nabena wanda yayi nuni ga hakan a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, yayin da yake hira da manema labarai a Abuja, yayi kira ga Sufeto-Janar na yan sanda, Mista Adamu Mohammed da ya haramta shigar tsaro na jihar, Operation Doo Akpo bisa zargin hada kai da gwamnatin jihar wajen cin mutunci da kuma razana yan adawa.

Mataimakin sakataren labaran wanda yayi magana akan lamarin tashin hankalin da aka samu a babban Birnin jihar Bayelsa, Yenagoa a ranar Litinin, bayan rikicin da aka samu a majalisar dokokin jihar, yayi zargin cewa wani babban jami'in jihar na haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar.

KU KARANTA KUMA: Babu bayyananen hujjar cewa Maina ya saci kudi - Lauya

Yace yana da bayanai aun dogaro cewa wasu mutane a cikin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar Bayelsa, sun shirya yan daba dauke da makamai daga jihohin ketare don hana zaman lafiya a jihar kafin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel