Tirkashi: Wani Sanata ya tona asirin yadda Sojoji ke taimakawa masu garkuwa da mutane a Najeriya

Tirkashi: Wani Sanata ya tona asirin yadda Sojoji ke taimakawa masu garkuwa da mutane a Najeriya

- Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa yanzu sojoji ne ke taimakawa 'yan ta'adda a kasar nan

- Ya bayyana cewa maimakon da sune suke kokarin ganin sun kawo karshen matsalar ta'addanci a kasar nan

- Ya ce ya kamata gwamnati ta tashi tsaye domin kawo karshen ta'addanci a kasar nan

Sanata mai wakiltar jihar Abia ta Kudu, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya zargi sojoji da taimakawa masu garkuwa da mutane, ba kamar da ba da suke kokarin ganin sun kawo karshen su.

Kamar yadda jaridar Information Nigeria ta ruwaito, Sanatan yayi wannan zargi ne a lokacin da yake magana dangane da matsalar tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja a lokacin da aka ta so da maganar a majalisa jiya Laraba.

A cewar shi, matsalar rashin tsaro a Najeriya, yana nuna cewa kasar na cikin babbar matsala wacce take bukatar a tsaya a lura a nemo mafita a kanta.

Abaribe ya ce: "Babu abinda muke yi in banda tashi tsaye muyi magana akan lamarin, kamar yadda nake tsaye a gabanku yau, ban sani ba amma zan iya cewa ya kamata mu tashi mu dauki mataki a kan wannan lamarin."

KU KARANTA: An bayyana shugaba Buhari da shugaban 'yan Boko Haram Abubakar Shekau a cikin jerin manyan Musulmai na duniya

"Ba zan manta ba a shekarar 2008 na taba kawo wannan maganar a lokacin da muke fama da matsalar masu garkuwa da mutane a jihar Abia, hakan ya saka aka aika da sojoji domin su kawo karshen 'yan ta'addar."

"Amma kuma yanzu sojojin da ya kamata su kawo karshen wannan matsalar sune suke taimakawa masu garkuwa da mutanen. Muna cikin babbar matsala, muna yiwa iyalan mutanen da aka kashe ta'aziyya."

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin abokan shi sun daina bin hanyar Abuja zuwa Kaduna saboda matsalar tsaro, inda ya kara da cewa: "Hakan na nufin mun bar 'yan ta'addar suyi abinda suka ga dama, wasu gwamnonin ma har sunje suna neman sulhu da 'yan ta'addar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel