Babu bayyananen hujjar cewa Maina ya saci kudi - Lauya

Babu bayyananen hujjar cewa Maina ya saci kudi - Lauya

Wani lauyan kare hakkin dan Adam, Frank Tietie, ya bayyana cewa babu wani hujja da za a tabbatar da cewa tsohon shugaban fansho, Abdulrasheed Maina, ya saci kowani kudi.

Mista Tietie ya fadi hakan ne yayinda yake martani ga kamun Maina a ranar Laraba.

Ya kuma bayyana cewa yana da yakini akan cewa da wannan kamun, yan Najeriya za su iya ganin karshen abunda ke lullube a badakalar Maina.

Tietie wanda ya yarda cewar tsohon shugaban na fansho ya ci moroyar kariya sosai, ya kuma bayyana cewa yana burin “dukkanin wadanda ke neman shi, wadanda ke tsoronsa a yanzu za su fito su fuskance shi sannan a bashi damar da zai fadi dukkanin gaskiya.”

A watan Nuwamba 2015 ne hukumar EFCC ta kaddamar da neman Maina ruwa a jallo kan zargin damfara naira biliyan biyu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta taya Tambuwal murna, tayi watsi da hukuncin kotun zabe a Plateau da Kano

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar tsaro na sirri ta tabbatar da kamun Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho. Peter Afunanya, kakakin rundunar ya tabbatar da kamun a wani jawabi da ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Yace an kama Maina ne a wani otel a Abuja a ranar 30 ga watan Satumba, 2019, cewa dansa yayi kokarin bude wuta akan jami’an DSS da suka aiwatar da aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel