Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)

Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, a ziyarar da ya kai kasar domin tattaunawa da takwararsa kan kisan yan Najeriya da wasu bakaken fata a kasar.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya da wasu kasashen Afrika a kasar Afrika ta kudu, ya yi kira da gwamnatin kasar ta aiwatar da matakan da aka zayyana domin kiyaye gaba.

Buhari yace: "Ya kai shugaban kasa, mun yi Allah wadai da hare-hare da aka kaiwa yan Najeriya da yan wasu kasashen Afrika a kasar Afrika ta kudu. Sace-sace da shagunansu da kone-konen dukiyoyinsu."

"Hakazalika mun yi Allah wadai da hare-haren ramuwar gayya da aka kai kasuwannin yan kasar Afrika ta kudu a gida Najeriya. Mun dau matakai na hana faruwan irin haka a nan gaba."

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa kasar Afrika ta kudu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Afrika ta kudu a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2019 kan al'amarin kin jin bakin fata da ke addabi kasar Afrika ta kudu a makonnin bayan.

KU KARANTA: A sake mana malaman yaranmu, taimaka mana suke - Iyayen yaran Islamiyyan Kaduna sun koka

Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa (Kalli hotunan)
Yanzu-yanzu: A Afrika ta kudu, Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel