A sake mana malaman yaranmu, taimaka mana suke - Iyayen yaran Islamiyyan Kaduna sun koka

A sake mana malaman yaranmu, taimaka mana suke - Iyayen yaran Islamiyyan Kaduna sun koka

Daya daga cikin iyayen yaran da akayi ikirarin cetowa daga makarantar tarbiyya a unguwar Rigasan jihar Kaduna ta ce babu wani abin aibantawa a makarantar kamar yadda ake yayatawa. Ta ce makarantar saita yaran da suka fara kangarewa ne.

A wannan hira da tayi da jaridar Punch, ta bayyana cewa za suyi tofin Allah tsine kan gwamnatin idan ba’a saki malamansu ba.

Ga yadda hirar ta kaya:

Yaya kika ji lokacin da kike kai danki makarantar?

Yarona na shekara 12 na kaishi makarantar kuma shekarunshi hudu kenan. Bai taba kawo kara cewa ana musu wani abu ba.

Kina cikin iyaye matan da suka yi zanga-zanga duk da cewa jama’a sun gani cewa halin da ake karantar da yaran na da tsanani, me yasa kukayi zanga-zanga?

Na shiga zanga-zangan ne saboda yarona bai taba kukan an zalunceshi ba. Na kan je makarantan in dubashi.

Amma yan sanda sun zargin shugabannin makarantar da karantar da su cikin hali mara dadin gani, me zakice game da haka?

Duk karerayi ne. Abinda yan sanda basu sani ba shine makarantar na kawo likitoci suna dubasu lokaci bayan lokaci. Shin yan sandan sun fi mu son yaranmu ne

Shin za ki mayar da yaranki makarantar tarbiyya duk da abinda ya faru?

Me zai hana? Zan mayar da shi. Nima dalibar makarantar ce. Munada sashen mata da muke zuwa karatu. Idan makarantar babu kyau da na sani.

Wasu yaran sun ce ana lalata da su. Shin kin taba jin haka daga bakin danki?

Kamar yadda na fada, duk karerayi ne. Zamu mutu kuma zamuyi hisabin ayyukanmu.

Shin za kiyi kiraga sakin malaman makarantan dake hannun hukuma?

Kwarai kuwa. Dalili shine shugaban makarantan na taimaka mana wajen tarbiyyan yaranmu bisa ga koyarwan addinin Musulunci. A sake mana su kuma su cigaba da ayyukansu na kwarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel