Ma’aikata 2 sun nemi bada cin hanci don hana binciken N35m a JAMB - Shaida

Ma’aikata 2 sun nemi bada cin hanci don hana binciken N35m a JAMB - Shaida

Bayanai su na cigaba da fitowa a game da wasu kudi da su ka yi dabo a hukumar jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare na JAMB. A baya, ma’aikatan sun ce Macijiya ce ta hadiye kudin.

Yanzu haka an samu labarin yadda babban jami’in da ke kula da harkar kudi a hukumar JAMB na reshen Makurdi, Samuel Saleh Umoru da kuma wata karamar Ma’aikaciya su ka nemi su hana binciken.

Saleh Umoru da Abokiyar aikinsa Philomina Chieshe sun yi kokarin biyan jami’in da ke bin diddikin kudi a ofishin JAMB Mallam Ibrahim Oba, cin hanci domin ya fasa binciken da aka sa shi.

Kamar yadda Shaidan farko da masu kara su ka gabatar ya bayyana, an yi wa ma’aikacin tayin N50, 000.00 da nufin ya janye binciken da zai tona masu asiri. Wannan shaida shi ne Patrick Obilo.

Mista Patrick Obilo ya sanar da babban kotun tarayya da ke zama a Maitama cewa Umoru da Chieshe wanda ake zargi sun yi kokarin ba Ibrahim Oba kudi saboda ya rufe ta’adin da su ka yi a hukumar.

KU KARANTA: Mai binciken kudi a APC ya zama Shugaban hukumar NIWA

Obilo ya yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin 30 ga Watan Satumban 2019 lokacin da wani Lauyan hukumar EFCC Ekele Iheanacho ya yi masa tambayoyi yayin da ake shari’a a gaban kuliya.

An tura Oba zuwa ofishin hukumar da ke Makurdi ne a 2016 domin ya yi binciken da aka saba a game da kudin da hukumar ta kashe, a nan ne Chieshe ta kawowa Oba kudi a cikin wata ambula.

Shaidan ya fadawa kotu cewa bayan Chieshe ta kawowa wannan kudi N50, 000 daga Mai gidanta Umoru, sai ta nemi Oba ya tattara ya koma Abuja wanda shi kuma ya kai karar abin da ya faru.

Bayan kukan da Oba ya kai ne, wani Mai gidansa a Hedikwata ya canza shi da Peter Obilo wanda ya ke bada shaida. Da zuwansa ya gano an wawuri N35, 480, 000 inda yanzu ake shari’a a kansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel