PDP ta taya Tambuwal murna, tayi watsi da hukuncin kotun zabe a Plateau da Kano

PDP ta taya Tambuwal murna, tayi watsi da hukuncin kotun zabe a Plateau da Kano

- Jam'iyyar PDP ta taya Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal akan nasarar da yayi a kotun zaben gwamna

- Ta bayyana hukuncin a matsayin nasara ga damokradiyya da kuma muradin mutane

- Sai dai kuma jam’iyyar tayi watsi da hukuncin kotun zaben gwamna a jihohin Kano da Plateau

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, ta taya Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal akan nasarar da yayi a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna na Sokoto, wacce ta jaddada zabensa.

A Wani jawabi daga babban sakataren labaran jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, zuwa ga manema labarai, jam’iyyar ta bayyana hukuncin a matsayin nasara ga damokradiyya da kuma muradin mutane.

Jam’iyyar ta bayyana cewa nasarar Gwamna Tambuwal a zaben ya tabbatar da aminta da tsarin shugabancinsa da kuma jajircewarsa wajen cigaban jihar da kuma tallafawa mutane.

Sai dai kuma jam’iyyar tayi watsi da hukuncin kotun zaben gwamna a jihohin Kano da Plateau.

KU KARANTA KUMA: Diban ma'aikata: Gwamnatin Kaduna ta saki sunayen mutane 13,700

Ta kuma bukaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar da kada su cire tsammani domin ba kotun zaben bane karshe inda ta kara kara da cewa gaskiya zata yi halinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel