Shugaban jam'iyyar SDP, Faforji ya yi murabus

Shugaban jam'iyyar SDP, Faforji ya yi murabus

- Shugaban jam'iyyar SDP na jihar Ogun ya yi murabus daga mukaminsa kuma ya fice daga jam'iyyar

- Dakta Bayo Faforji ya ce ya fice daga jam'iyyar ne sakamakon rashin gamsuwa da wasu akidojin jam'yyar da ya ga ba suyi dai-dai tasa akidar ba

- Kafin ficewarsa, a rika samun rashin jituwa tsakaninsa da wasu masu fada a ji a jam'iyyar

Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party a jihar Osun, Dakta Bayo Faforji a ranar Laraba ya mika takardan yin murabusa a matsayinsa na shugaba da kuma dan jam'iyyar ta SDP ga shugabanin jam'iyyar na kasa.

Faforji wanda ya jagoranci jam'iyyar ta SDP a zaben gwamnan 2018 yayin da Sanata Iyiola Omisore ya yi takarar a jihar ya dade yana sa-in-sa da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Wani sashi na cikin wasikar murabus din da Faforji ya aike wa shugaban jam'iyyar na kasa mai dauke da kwanan wata ranar 2 ga watan Oktoba ya ce, "Na fahimci cewa akwai banbanci tsakanin akidu na a matsayina na ciyaman da kuma dan jam'iyyar da wasu akidun jam'iyyar kuma ina fatan kiyaye aikidun nawa muddin dai Allah ya bar ni da rai."

The Punch ta ruwaito cewa Faforji ya tabbatar da murabus din nasa amma bai yi wani karin haske ba bisa dalilan da yasa ya yi murabus din.

A baya an samu rigingimu na shugabancin jam'iyyar ta kasa tsakanin Farfesa Jerry Gana da tsohon gwamna Donald Duke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel