CLO: Nadin Moghalu a matsayin Shugaban NIWA ya yi wa Ibo dadi

CLO: Nadin Moghalu a matsayin Shugaban NIWA ya yi wa Ibo dadi

A cikin farkon makon nan ne mu ka samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr. George Moghalu a matsayin shugaban hukumar NIWA mai kula da kan ruwan Najeriya.

Wannan nadin mukami da ya yi, ya sa wasu musamman Kabilar Ibo su na ta zubawa shugaban kasar yabo. Kamar yadda The Nation ta rahoto, wata kungiya ta fitar da jawabi a game da nadin.

Kungiyar nan ta Civil Liberties Organisation mai zaman kan-ta, ta ce mukamin da aka ba Moghalu a NIWA shi ne babbar kyautar da Buhari ya ba Yankin Ibo a ranar murnar ‘yancin-kai.

Shugaban wannan kungiya ta CLO na reshen jihar Anambra, Vincent Ezekwueme, yake cewa za su cigaba da godewa shugaban kasar a kan wannan abu da ya yi masu na kokarin jawo su a jika.

“Wannan abin a yaba kuma ayi murna ne ga mutanen Kudu maso Gabas da sauran Najeriya. Wannan shi ne babbar kyautar da aka yi wa Kudu maso Gabas a Ranar bikin murnar ‘yanci.”

KU KARANTA: Buhari ya dauki wasu Gwamnoni da Ministoci zuwa Afrika ta Kudu

Jawabin na Vincent Ezekwueme ya kara da cewa: “Shugaban kasar ya bada damar babbako da tashar ruwan Onitsha wanda ya sukurkuce.” CLO ta kuma yi kira ga Moghalu ya yi abin burgewa.

Moghalu a matsayinsa na mai kishi kuma wanda ya san ya kamata, ga gaskiya da bauta da kuma kan-kan da kai, dole ya sa al’umma a gabansa ta hanyar tada tashar Onitsha domin a samu aiki.”

Ezekwueme ya nemi sabon shugaban na NIWA ya dage wajen ganin Ibo su ji ana yi da su. A karshe CLO ta roki ya ba dangin tsohon Abokin siyasarsa Chuba Okadigbo mukami a gwamnati.

Marigayi Chuba Okadigbo shi ne ya tsayawa Buhari a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023. Shi kuwa George Moghalu ya na cikin manyan Jiga-jigan APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel