Za mu dawo da shingen shiga cikin Gari a titunan Najeriya – Inji Fashola

Za mu dawo da shingen shiga cikin Gari a titunan Najeriya – Inji Fashola

Mun samu labari gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala duk wani shirye-shirye da ake bukata na dawo da sa iyakar shiga cikin Gari a manyan hanyoyin da ke cikin fadin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ya kyankyasa cewa za a dawo da wannan tsari kwanan nan. A Ranar Laraba 2 ga Oktoba, Fashola ya ce sun gama shirin.

Bayan kammala taron majalisar zartarwa na wannan makon, Mista Babatunde Raji Fashola ya fadawa ‘yan jarida cewa babu wani dalili na daina tare Matafiya a kan manyan titunan kasar.

“Bari in yi wani karin haske kan wadannan kofofin shiga gari; babu dalilin da zai hana mu yin shinge; babu wani dalili. Gwamnatin tarayya ta taba kawo tsarin daina karbar kudi.” Inji Fashola.

KU KARANTA: Masu amfani da salula za su fara biyan harajin waya da kallon talabijin

Ministan kasar ya cigaba da cewa: “Amma babu dokar da ta ce a cire shingen kan hanyoyin da ke Najeriya. Mu na sa rai mu dawo da karbar kudi a kan tituna; mun kammala zanen gine-ginen”

Fashola ya ce yanzu an kammala aiki kan irin ginin da za a yi, da kuma kayan da za a yi amfani da su da yadda aikin zai kasance. Abin da ya rage shi ne kurum abubuwan da za ayi la’akari da su.

Ministan ayyukan ya nuna cewa su na kokarin ganin yadda za a yi watsi da batun karbar kudi a kan hanyoyin tare da ganin ba a batawa mutane lokaci a sakamakon binciken da za a rika yi.

“Mu na kuma bukatar karin fili domin a gina shinge mai layi 10. Abin da wasu ke tunani shi ne da kudin da aka tara a kan titunan za a rika gyara hanyoyin. Ministan yace: “Wannan ba haka bane.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel