Dalilan da yasa kungiyoyin kwadago ke barazanar tafiya yajin aiki

Dalilan da yasa kungiyoyin kwadago ke barazanar tafiya yajin aiki

- Kungiyar Kwadago ta yi barazanar fara yin yakin aikin yi na gama gari a ranar 16 ga watan Oktoba

- Kungiyar za tayi hakan ne saboda gazawar gwamnatin tarayya na cika wasu ka'idoji game da karin albashi mafi karanci

- Shugaban kungiyar na kasa ya ce sun nuna hakuri da juriya amma gwamnatin ba ta cika alkawurran da ta dauka ba

A ranar Laraba ne kungiyar kwadago ta yi barazanar fara yajin aiki a fadin kasar nan zuwa 16 ga watan Oktoba, matukar suka kasa daidaitawa akan sabon karancin albashi a taron da zasu kara yi da gwamnatin tarayya.

Kungiyar kwadagon da kungiyar kasauwanci ta kasa, a taron da suka yi kungiyar ciniki ta hadaka, sun ja kunnen cewa, kungiyar kwadago ba zata bada tabbacin cigaba da aiki ba matukar gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatunsu.

Ma'aikatan gwamnati a Najeriya suna cikin damuwa saboda gazawar gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago wajen kawo karshen tattaunawarsu akan sabon karancin albashin da aka maida doka tun watanni shida da suka gabata.

DUBA WANNAN: Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

A takardar da shugaban NLC, Ayuba Wabba, shugaban TUC, Quadri Olaleye da Simon Anchaver, mukaddashin shugaban JNPSNC, sun ce kungiyoyin kwadagon sun gawada hakurinsu da juriya ga gwamnatin tarayya.

"Duk da kishin kasa da muka nunawa gwamnati, ta nuna cewa zata iya kara 11% na albashin ne ga ma'aikata masu mataki na 7 zuwa 14 inda kuma zata iya biyan ma'aikata na mataki 15 zuwa 17 karin 6.5%."

Kamar yadda suka ce, darajar Naira ta sauka daga N150 da take daidai da dala daya a 2011 zuwa N360 da ta zamo daidai da dala daya a 2019; faduwar kashi 140 na kudin Najeriyar.

Shuwagabannin kungiyar sun ce, tun bayan zartar da tsohon karancin albashi na N18,000, an tilasta ma'aikata wajen fuskantar hauhawan kudaden kayayyaki.

Kudin litar man fetur da yake N87 ya daga zuwa N145 wanda ke nufin karin 60% na asalin kudin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel