Kudirin Majalisar Tarayya na so a sa haraji a kan GSM da Talabijin

Kudirin Majalisar Tarayya na so a sa haraji a kan GSM da Talabijin

Kudirin da ke nema a kawo haraji a cikin harkar sadarwa da kuma talabijin na tsarin satalayit ya tsallake matakin farko a gaban majalisar dattawan Najeriya kamar yadda mu ka samu labari.

A yau Alhamis, 3 ga Watan Oktoba 2019 aka rahoto cewa Sanatoci su na kokarin kawo wannan sabon salon haraji ne domin ya maye gurbin shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi na kara VAT.

Sanata Ali Mohammed Ndume shi ne wanda ya kawo wannan kudiri a zauren majalisar dattawan inda yake so a kawo sabon dokar haraji wanda za ta sa a fasa kara harajin da ake biya kan kaya.

Ali Mohammed Ndume ya yi magana da Manema labarai a majalusa jim kadan bayan kudirin ya yi zarcewar farko a zaure. Sanatan na APC ya ce karbar harajin wayar salula zai fi taimakawa.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya rantsar da sababbin masu ba shi shawara

Sanatan na Kudancin jihar Borno ya na da ra’ayin cewa kara harajin VAT zai sa kayayyaki su kara tsada a kasuwa, wanda hakan babban nauyi ne kan Talakawa wanda zai shafi tattalin arziki.

Wannan kudiri ya na neman ganin an sa harajin 9% a kan duk kudin da ake kashewa wajen wayar tarho da hawa yanar gizo. Gwamnati za ta rika karbar harajin ne daga kamfanonin sadarwa.

Harajin zai shafi kananan sakonni na SMS da kuma sakonni masu nauyi na MMS da abin da aka kashe wajen hawan shafin yanar gizo. Harajin zai kuma shafi gidajen talabijin da ke yanar gizo.

A wannan kudiri da Ali Ndume ya gabatar, hukumar FIRS mai karbar haraji ne aka ba alhakin kula da wannan haraji. FIRS za ta ba gwamnatin Najeriya abin da ta tara har da tarar da ta daura.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel