Diban ma'aikata: Gwamnatin Kaduna ta saki sunayen mutane 13,700

Diban ma'aikata: Gwamnatin Kaduna ta saki sunayen mutane 13,700

Gwamnatin jihar Kaduna ta saki sunayen mutane 13,700 daga cikin mutane 41,971 da ke neman aiki a hukumar diban ma’aikata na jihar.

Hadimin Gwamna Nasir El-Rufai na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Muyiwa Adekeye, a jiya Laraba yace jerin sunayen ya billo ne bayan an tantance kokarinsu a gwajin farko da aka yi na diban ma’aikatan.

Da yake bayani kan rabe-raben masu neman aikin, Adekeye yace an samu wadanda suka nemi aikin daga jihohi 36 da kuma birnin tarayya.

Yace jihar Kaduna ce ta samar da mutane 32,143 daga cikin 41,971 dake neman aikin, sai Kogi dake da 1,265, Benue, 733 da birnin tarayya wacce ke da 730; yayinda akwai mutane 516 daga jihar Lagas, 147 daga Anambra da kuma 18 daga Bayelsa.

“A karshen gwajin matakin farko, mutane yan shekara 35 ko kasa da aka sun kasance kaso 78.48% na wadanda aka saki sunayensu, yayinda sabon shiga suka fi yawa kusa 7,724. Jihar Kaduna na da mutum 10,696 cikin 13,700 da aka saki sunayensu,” inji shi.

KU KAANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada sabon manajan darakta na NIWA

Yayi bayanin cewa masu neman aikin 41,971 sun gabatar da wani muqala da farko a yanar gizo sannan a duba su don ganin wadanda suka yi satar amsa da kuma tsarin Turanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel