Tsugunne ba ta kare ba a jihar Kano: Mun daukaka kara a kotun Kaduna - Abba Gida-Gida

Tsugunne ba ta kare ba a jihar Kano: Mun daukaka kara a kotun Kaduna - Abba Gida-Gida

- Dan takarar gwamna na babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yayi magana akan shari'ar da kotu ta yanke jiya a jihar Kano

- Dan takarar ya bayyana cewa yanzu haka ya daukaka kara domin ya kalubalanci kotu akan tabbatar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar

A wata hira da yayi da BBC, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya bayyana cewa tuntuni lauyoyinsa suka cika dukannin takardun da ake bukata domin daukaka kara.

"Mun daukaka kara domin kwato hakkin al'ummar jihar Kano," in ji shi.

Alkalin kotun kararrakin zaben ta jihar Kano, mai shari'a Halima Shamaki ita ce ta yi watsi da karar da dan jam'iyyar adawar ta PDP ya shigar a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar nan, sannan kuma ta bayyana gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar ta Kano.

Alkalin kotun ta yi watsi da shari'ar ne bayan ta bayyana cewa dan jam'iyyar adawar ta PDP ya kasa gamsar da kotu cewa jam'iyyar APC ta yi magudi a zaben da aka gabatar a ranar 23 ga watan Maris.

KU KARANTA: Maganar tazarcen da Buhari yake yi akwai lauje cikin nadi - Buba Galadima

Sai dai kuma alkalin kotun ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ta na da hurumin da za ta daukaka kara zuwa kotun koli idan har hukuncin da ta yanke bai yi musu ba.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sun tanadi manyan lauyoyi guda bakwai da kuma kanana sama da guda arba'in wadanda za su kalubalanci wannan hukunci da kotun kararrakin zaben ta yanke. "Muna da yakinin za mu samu nasara," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel