Har gobe ni mai biyayya ne ga Buhari - Osinbajo

Har gobe ni mai biyayya ne ga Buhari - Osinbajo

Ana tsaka da yada rahotannin baraka a fadar shugaban kasa, mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sha alwashin yin biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wani mujalla mai taken “This is Nigeria” wanda aka kaddamar a bikin cin abincin dare na ranar damokradiyya, a ranar 1 ga watan Oktoba a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Osinbajo ya taya Buhari, uwargidarsa da babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu murna.

Osinbajo ya jaddada biyayyarsa ga shugaba Buhari inda sakon ke cewa; “Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na taya yan Najeriya murnar zagayowar ranar yanci karo na 59; yayinda ya sha alwashin biyayya ya shugaban kasa Muhammadu Buhari."

Ya bayyana Buhari a matsayin “ubangida nagari sannan Ina ganin abun burgewa ne ganin Ina yiwa Najeriya hidima a karkashinsa. Ya zama dole gare ni na yi cikakken biyayya ga shugaba Buhari da Najeriya kamar yadda na dauki alkawarin kasancewa tare dashi a koda yaushe, yayinda nake bayar da gudunmawana domin cigaban Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin ruwa tara diban sabbin ma’aikata masu digiri da HND

“Ina kira ga dukkanin yan Najeriya da su marawa shugaba Buhari baya yayinda yake jagorantarmu wajen gina Najeriya ta yadda za ta bunkasa da kara karfi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel